Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions

636 ayoyi · 252 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”

  2. Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce, “Hadaya da sadaka kam ba ka so, sai dai ka tanadar mini jiki;

  3. hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.

  4. Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”

  5. Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa,

  6. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.”

  7. Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.”

  8. Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”

  9. Amma, “Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan ji daɗinsa ba.”

  10. ko da yake Allah ya ce masa, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.”

  11. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,

  12. domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.”

  13. A lokacin nan muryarsa ta jijjiga duniya, amma yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau sau ɗaya tak zan ƙara jijjiga ba duniya kaɗai ba, amma har ma da sammai.”

  14. Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”

  15. Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”

  16. Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.

  17. In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.

  18. Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.

  19. Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.

  20. Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girman kai amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.”

  21. gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”

  22. Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,

  23. amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

  24. Gama a cikin Nassi an ce, “Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona, zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja, wanda kuma ya dogara gare shi ba zai taɓa kunyata ba.”

  25. A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini,