Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Hebrews 3:7, »To day if ye will hear his voice...«

10 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Hebrews 3:7, »To day if ye will hear his voice...«

  1. gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,

  2. “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,

  3. inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.

  4. Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’

  5. Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

  6. Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,

  7. kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,

  8. inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.

  9. Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’

  10. Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.”