- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 6 BC – AD 30
The Life of Jesus
The eternal Son of God enters history: born in Bethlehem, baptized in the Jordan, crucified at Golgotha, raised on the third day.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Mattiyu 1:1kusan 26 M.
Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.
- Mattiyu 1:2kusan 26 M.
Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yaƙub, Yaƙub ya haifi Yahuda da ’yan’uwansa,
- Mattiyu 1:3kusan 26 M.
Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu; Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Ram,
- Mattiyu 1:4kusan 26 M.
Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,
- Mattiyu 1:5kusan 26 M.
Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse,
- Mattiyu 1:6kusan 26 M.
Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.
- Mattiyu 1:7kusan 26 M.
Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa,
- Mattiyu 1:8kusan 26 M.
Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yehoram, Yehoram ya haifi Azariya,
- Mattiyu 1:9kusan 26 M.
Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,
- Mattiyu 1:10kusan 26 M.
Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya,
- Mattiyu 1:11kusan 26 M.
Yosiya kuma ya haifi Yekoniya da ’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.
- Mattiyu 1:12kusan 26 M.
Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon. Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,
- Mattiyu 1:13kusan 26 M.
Zerubbabel ya haifi Abiyud, Abiyud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor,
- Mattiyu 1:14kusan 26 M.
Azor ya haifi Zadok, Zadok ya haifi Akim, Akim kuma ya haifi Eliyud,
- Mattiyu 1:15kusan 26 M.
Eliyud ya haifi Eleyazar, Eleyazar ya haifi Mattan, Mattan ya haifi Yaƙub,
- Mattiyu 1:16kusan 26 M.
Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.
- Mattiyu 1:17kusan 26 M.
Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.
- Mattiyu 1:18kusan 26 M.
Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
- Mattiyu 1:19kusan 26 M.
Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.
- Mattiyu 1:20kusan 26 M.
Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne.
- Mattiyu 1:21kusan 26 M.
Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
- Mattiyu 1:22kusan 26 M.
Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa,
- Mattiyu 1:23kusan 26 M.
“Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).
- Mattiyu 1:24kusan 26 M.
Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa.
- Mattiyu 1:25kusan 26 M.
Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.