Skip to content

David

968 ayoyi · 40 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci David

Tace bisa littafi
  1. Matan da suke zama a wurin suka ce, “Na’omi ta sami yaro.” Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda.

  2. Obed ya haifi Yesse, Yesse kuwa ya haifi Dawuda.

  3. Saboda haka Sama’ila ya ɗauko ƙahon nan da yake da mai ya shafe Dawuda a gaban ’yan’uwansa. Daga wannan rana kuwa ruhun Ubangiji ya sauko wa Dawuda da iko. Sai Sama’ila ya koma Rama.

  4. Sai Shawulu ya aiki manzanni zuwa wurin Yesse ya ce, “Ka aiko mini da ɗanka Dawuda wanda yake kiwon tumaki.”

  5. Saboda haka Yesse ya ɗauki jaki tare da burodi da ruwan inabi da ɗan ƙarami bunsuru ya ba wa ɗansa Dawuda yă kai wa Shawulu.

  6. Dawuda ya isa wurin Shawulu ya shiga hidimarsa. Shawulu kuwa ya so shi ƙwarai da gaske. Dawuda ya zama ɗaya daga cikin masu sanya sulke.

  7. Sa’an nan Shawulu ya aika saƙo wurin Yesse cewa, “Ka bar Dawuda yă yi mini hidima domin ina jin daɗinsa ƙwarai.”

  8. Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.

  9. To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.

  10. Dawuda shi ne ɗan autansu. Manyan ’yan mazan nan uku suka bi Shawulu.

  11. Amma Dawuda yakan tafi sansanin Shawulu lokaci-lokaci yă kuma koma Betlehem don yă yi kiwon tumakin mahaifinsa.

  12. Yesse ya ce wa ɗansa Dawuda, “Ka ɗauki wannan gasasshen hatsi da waɗannan curin burodi goma, ka kai wa ’yan’uwanka a sansani da sauri.

  13. Kashegari da sassafe, Dawuda ya tashi ya bar tumakinsa wa wani yă lura da su, sai ya ɗauki kayansa, ya kama hanya kamar yadda Yesse ya umarce shi. Ya isa sansanin daidai sa’ad da rundunar tana fitowa zuwa bakin dāgā, suna kirarin yaƙi.

  14. Dawuda ya bar kayansa a wajen wani mai lura da kaya, sai ya ruga zuwa bakin dāgā yă gai da ’yan’uwansa.

  15. Da yana magana da su sai Goliyat, jarumin nan Bafilistin daga Gat ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya tā da murya kamar yadda ya saba. Dawuda kuwa ya ji shi.

  16. Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?”

  17. Da wansa Eliyab, ya ji yana magana da mutanen, sai ransa ya ɓace ƙwarai saboda fushi, sai ya ce wa Dawuda, “Me ka zo yi a nan? Wa kuma ka bar wa ’yan tumakin a jeji? Na san ka da taurinkai, da kuma mugun hali. Ka zo nan ne don ka yi kallon yaƙi kawai.”

  18. Dawuda ya ce, “To, yanzu me na yi? Ba zan ma yi magana ba?”

  19. Aka ji abin da Dawuda ya ce, aka kuwa gaya wa Shawulu, Shawulu kuma ya aika a kawo shi.

  20. Da Shawulu ya tambayi Dawuda, sai Dawuda ya ce masa, “Kada kowa yă damu saboda wannan Bafilistin. Bawanka zai je yă yi faɗa da shi.”

  21. Shawulu ya ce, “Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai.”

  22. Amma Dawuda ya ce wa Shawulu, “Bawanka yana kiwon tumakin mahaifinsa. Sa’ad da zaki ko beyar ta zo ta kama tunkiya, ta tafi da ita.

  23. Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin.” Shawulu ya ce wa Dawuda, “Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai.”

  24. Sai Shawulu ya kawo kayan yaƙinsa ya sa wa Dawuda. Ya sa masa hular kwanon da aka yi da tagulla a kansa, ya kuma sa masa rigar ƙarfensa.

  25. Dawuda ya ɗaura māshin Shawulu a sulken, ya yi ƙoƙari yă zaga, sai ya ji ba zai iya ba saboda bai saba ba. Ya cewa Shawulu, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, domin ban saba ba.” Don haka ya tuɓe su.