Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple

365 ayoyi · 72 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.”

  2. “Je ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, kai ne za ka gina mini gida in zauna?

  3. Ban taɓa zama a gida ba tun daga ranar da na fito da Isra’ilawa daga Masar har yă zuwa yau. Ina dai kai da kawowa a tenti, a matsayin mazaunina.

  4. A cikin kaiwa da kawowar da nake yi cikin dukan Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani shugabanninsu wanda na umarta su lura da mutanena Isra’ila, “Don me ba ku gina mini mazauni da katakon al’ul ba?” ’

  5. “Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila.

  6. Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma kawar da dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka yă shahara kamar sunayen shahararrun mutanen duniya.

  7. Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu.

  8. Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada.

  9. “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

  10. “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”

  11. Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”

  12. Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir.

  13. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”

  14. A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata.

  15. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.

  16. Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya.

  17. Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin.

  18. Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun.

  19. Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai,

  20. A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.

  21. Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne.

  22. Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma.

  23. Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin.

  24. A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe.

  25. Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali.