Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The First Temple: Zion
Ayoyi game da Zion
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Na ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ina misalin kyan wurin zamanka, Ya Ubangiji Maɗaukaki!
Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai.
Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.
Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela
Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka, waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.
Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka, sukan mai da shi wurin maɓulɓulai; ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.
Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.