Skip to content

Hezekiah

116 ayoyi · 5 'yan gida

An kuma san shi da: Ezekias

Ayoyin da suka ambaci Hezekiah

Tace bisa littafi
  1. Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi.

  2. A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki.

  3. A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.

  4. A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila.

  5. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su.

  6. Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda.

  7. Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.

  8. A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.

  9. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.

  10. Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?

  11. Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?

  12. Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba.

  13. Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’

  14. “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa,

  15. har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’

  16. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.

  17. Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji.

  18. Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.

  19. Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya,

  20. To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa,

  21. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’

  22. Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji.

  23. Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.

  24. Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya.

  25. A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”