Skip to content

Ahaz

37 ayoyi · 4 'yan gida

An kuma san shi da: Achaz

Ayoyin da suka ambaci Ahaz

Tace bisa littafi
  1. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi.

  2. A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki.

  3. Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba.

  4. Sai Rezin sarkin Aram, da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su kai wa Urushalima hari, suka kuma kewaye Ahaz, amma ba su iya shan ƙarfinsa ba.

  5. Ahaz ya aika a faɗa wa Tiglat-Fileser sarkin Assuriya cewa, “Ni abokin tarayyarka ne kuma mai dogara da kai. Ka haura ka cece ni daga hannun sarkin Aram da hannun sarkin Isra’ila waɗanda suke kawo mini hari.”

  6. Ahaz ya ɗauki azurfa da zinariyar da suke a haikalin Ubangiji da suke kuma a ma’ajin fada ya aika wa sarkin Assuriya kyauta.

  7. Sa’an nan sarki Ahaz ya tafi Damaskus don yă sadu da Tiglat-Fileser sarkin Assuriya. Da ya kai can sai ya ga wani bagade a Damaskus, sai ya aika wa Uriya firist, da siffar bagaden, da fasalinsa, da cikakken bayanin bagaden.

  8. Saboda haka Uriya firist ya gina bagaden bisa ga tsarin da Sarki Ahaz ya aika masa daga Damaskus, ya kuma gama shi kafin Sarki Ahaz yă dawo.

  9. Sarkin Ahaz ya umarci Uriya cewa, “A kan babban sabon bagade, ka miƙa hadayar ƙonawa ta safe, da hadayar hatsi ta yamma, da hadayar sarki ta ƙonawa da hadayarsa ta hatsi, da hadaya ta dukan jama’ar ƙasar, tare da hadayan hatsinsu da kuma ta sha. Ka yayyafa jinin hadayun ƙonawa a kan bagade. Amma zan yi amfani da bagaden tagulla don neman bishewa.”

  10. Uriya firist kuwa ya yi duk abin da Sarki Ahaz ya umarta.

  11. Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse.

  12. Game da sauran ayyukan mulkin Ahaz, abubuwan da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  13. Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi da su a Birnin Dawuda. Hezekiya ɗansa kuma ya gāje shi.

  14. A shekara ta goma sha biyu ta mulkin Ahaz sarkin Yahuda, Hosheya ɗan Ela ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki na shekara tara.

  15. A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki.

  16. Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina.

  17. Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron.

  18. da Ahaz, da Hezekiya da Manasse,

  19. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  20. Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba.

  21. A lokacin nan Sarki Ahaz ya aika wurin sarkin Assuriya neman taimako.

  22. Ubangiji ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz sarkin Isra’ila, gama ya hadasa mugunta a Yahuda kuma ya kasance marar aminci ga Ubangiji.

  23. Ahaz ya ɗauki waɗansu abubuwa daga haikalin Ubangiji da kuma daga fadan sarki da kuma daga sarakuna, ya ba da su ga sarkin Assuriya, amma wannan bai taimake shi ba.

  24. Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji.

  25. Ahaz ya tattara kayayyaki daga haikalin Allah ya kwashe su. Ya kulle ƙofofin haikalin Ubangiji ya kakkafa bagadai a kowace kusurwa a titin Urushalima.