Skip to content

Jotham

20 ayoyi · 3 'yan gida

An kuma san shi da: Joatham

Ayoyin da suka ambaci Jotham

  1. Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.

  2. Azariya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi kusa da su a Birnin Dawuda. Yotam ɗansa, kuma ya gāje shi.

  3. Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya.

  4. A shekara ta biyu ta mulkin Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Uzziya sarkin Yahuda ya fara mulki.

  5. Game da sauran ayyukan mulkin Yotam da aikin da ya yi, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.

  6. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda, birnin mahaifinsa. Ahaz ɗansa kuma ya gāje shi.

  7. A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki.

  8. da Amaziya, da Azariya, da Yotam,

  9. Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.

  10. Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.

  11. Uzziya ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi kusa da su a fili don binnewar da take ta sarakuna, domin mutane sun ce, “Yana da kuturta.” Sai Yotam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  12. Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok.

  13. Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa.

  14. Sauran ayyuka a mulkin Yotam, haɗe da dukan yaƙe-yaƙensa da waɗansu abubuwan da ya yi, suna a rubuce a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda.

  15. Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.

  16. Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.

  17. Sa’ad da Ahaz ɗan Yotam, ɗan Uzziya, yake sarkin Yahuda, Sarki Rezin na Aram da Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila suka haura don su yaƙi Urushalima, amma ba su iya cinta da yaƙi ba.

  18. Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila.

  19. Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

  20. Azariya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya,