Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings

580 ayoyi · 175 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa.

  2. Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali

  3. don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.

  4. Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”

  5. Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.

  6. Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa.

  7. Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.

  8. Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.

  9. Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa.

  10. Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa.

  11. Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki.

  12. Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa.

  13. Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”

  14. A daidai wannan lokacin kuwa Shawulu yana dawowa daga gona tare da shanunsa na noma, sai ya ce, “Me ya faru, mutane suna kuka haka?” Sai suka faɗa masa abin da mutanen Yabesh suka faɗa musu.

  15. Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.

  16. Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.

  17. Ba lokacin yankan alkama ke nan ba? Zan roƙi Ubangiji yă aiko da tsawa da ruwan sama, za ku kuwa gane wace irin mugunta kuka yi a gaban Ubangiji sa’ad da kuka roƙa a ba ku sarki.

  18. Sai Sama’ila ya roƙi Ubangiji, a ranar kuwa Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama. Dukan mutane suka ji tsoron Ubangiji da kuma Sama’ila.

  19. Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”

  20. Sama’ila ya ce, “Kada ku ji tsoro.” Kun yi waɗannan mugunta duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta wa Ubangiji da dukan zuciyarku.

  21. Ya zauna a kujeransa inda ya saba zama kusa da bango yana fuskantar Yonatan, Abner kuma ya zauna kusa da sarki. Amma kujeran Dawuda ba kowa.

  22. Shawulu bai ce kome ba a ranar domin ya yi tsammani wataƙila wani abu ya faru da Dawuda ya mai da shi marar tsarki, tabbatacce ba shi da tsarki.

  23. Amma kashegari, rana ta biyu ga wata, kujeran Dawuda kuma ba kowa, sai Shawulu ya ce wa ɗansa Yonatan, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo cin abinci, jiya da yau ba?”

  24. Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala,

  25. sa’ad da wani mutum ya ce mini, ‘Shawulu ya mutu,’ yana tsammani ya kawo labari mai daɗi ne, na kama shi na kashe a Ziklag. Ladar da na ba shi ke nan saboda labarinsa!