Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings: Ahaziah

31 ayoyi · 175 fannoni

Ayoyi game da Ahaziah

Tace bisa littafi
  1. Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu.

  2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, domin ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa da na mahaifiyarsa, da kuma a hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi.

  3. Ya bauta, ya kuma yi wa Ba’al sujada, ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi, kamar yadda mahaifinsa ya yi.

  4. A shekara ta goma sha biyu ta Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya fara mulki.

  5. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya, jikanyar Omri, sarkin Isra’ila.

  6. Ya bi gurbin gidan Ahab, ya yi mugunta a gaban Ubangiji yadda gida Ahab ta yi, gama yana da dangantaka ta aure da gidan Ahab.

  7. Ahaziya ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot Gileyad. Arameyawa suka yi wa Yoram rauni;

  8. saboda haka Sarki Yoram ya koma zuwa Yezireyel don yă yi jinyar raunin da Arameyawa suka ji masa a Rama a yaƙinsa da Hazayel sarkin Aram. Sai Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda ya gangara zuwa Yezireyel yă dubi Yoram ɗan Ahab domin an yi masa rauni.

  9. Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi.

  10. Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ”

  11. Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.”

  12. Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”

  13. Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.”

  14. Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.

  15. Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?”

  16. Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!”

  17. Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa.

  18. Yehu ya ce wa Bidkar, hafsan keken yaƙinsa, “Ka ɗauke shi ka jefar a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Ka tuna yadda ni da kai muke a kekunan yaƙi a bayan Ahab mahaifinsa sa’ad da Ubangiji ya yi wannan annabci game da shi,

  19. ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.”

  20. Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.

  21. Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.

  22. (A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.)

  23. Mutanen Urushalima suka mai da Ahaziya, autan Yehoram, sarki a madadinsa, da yake ’yan hari, waɗanda suka zo tare da Larabawa cikin sansani, sun kashe dukan manyan ’ya’yansa. Saboda haka Ahaziya ɗan Yeroham sarkin Yahuda ya fara mulki.

  24. Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri.

  25. Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau.