Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings: Nadab
Ayoyi game da Nadab
Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu.
Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.
Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto.