Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kings: Shallum
Ayoyi game da Shallum
Shallum ɗan Yabesh ya zama sarki a shekara ta talatin da tara ta mulkin Uzziya sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki na wata ɗaya a Samariya.
Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.
Game da sauran ayyukan mulkin Shallum, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.