Tsallake zuwa abun ciki

Jeroboam

81 ayoyi · 4 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Jeroboam

Tace bisa littafi
  1. Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.

  2. To, Yerobowam mutum ne mai fasaha. Sa’ad da Solomon ya ga yadda matashin yake aiki da himma, sai ya sa shi yă lura da dukan aikin gandu na gidan Yusuf.

  3. Da Yerobowam ya fita Urushalima, sai annabi Ahiya, mutumin Shilo ya tarar da shi a hanya. Lokacin kuwa Ahiya yana saye da sabuwar riga, ba kowa a filin sai su biyu kaɗai.

  4. Sa’an nan ya ce wa Yerobowam, “Ɗauki gida goma wa kanka, gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce ke nan, ‘Duba, zan yage masarauta daga hannun Solomon in ba ka kabilu goma.

  5. Solomon ya yi ƙoƙari yă kashe Yerobowam, amma Yerobowam ya tsere zuwa Masar, zuwa wurin sarki Shishak, ya zauna a can sai bayan mutuwar Solomon.

  6. Sa’ad da Yerobowam ɗan Nebat ya ji labari (gama har yanzu yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon), sai ya dawo daga Masar.

  7. Saboda haka mutane suka aika Yerobowam yă zo, sai shi da dukan taron Isra’ila suka tafi wurin Rehobowam, suka ce masa,

  8. Bayan kwana uku, Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam yadda sarki ya faɗa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”

  9. Saboda haka sarki bai saurare mutane ba, gama wannan abin da ya faru daga wurin Ubangiji ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi wa Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya, mutumin Shilo.

  10. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ji Yerobowam ya dawo, sai suka aika, suka kira shi zuwa taro, suka kuma naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. Kabila Yahuda kaɗai ta kasance mai biyayya ga gidan Dawuda.

  11. Sai Yerobowam ya ƙara gina Shekem a ƙasar tudu ta Efraim, ya zauna a can. Daga can ya tafi ya gina Fenuwel.

  12. Yerobowam ya yi tunani a ransa ya ce, “Mai yiwuwa mulkin yă koma gidan Dawuda.

  13. Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi.

  14. Bisa ga umarnin Ubangiji, sai wani mutumin Allah ya zo daga Yahuda zuwa Betel, yayinda Yerobowam yake tsaye kusa da bagade don yă miƙa hadaya.

  15. Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba.

  16. Har ma bayan wannan, Yerobowam bai canja daga mugayen hanyoyinsa ba, amma ya ƙara naɗa firistoci domin masujadai da suke kan tuddai daga kowane irin mutane. Duk wanda ya so yă zama firist sai yă naɗa shi don aiki a masujadai da suke kan tuddai.

  17. Wannan ne zunubin gidan Yerobowam da ya kai ga fāɗuwarsa da kuma hallakarsa daga fuskar duniya.

  18. A lokacin Abiya, ɗan Yerobowam ya kamu da ciwo,

  19. sai Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tafi, ki ɓad da kama, don kada a gane ke a matsayin matar Yerobowam. Ki je Shilo. Annabi Ahiya yana a can, wannan wanda ya ce mini zan zama sarki a bisa wannan mutane.

  20. Saboda haka matar Yerobowam ta yi abin da ya faɗa, ta kuma tafi gidan Ahiya a Shilo. Yanzu dai Ahiya ba ya gani; idanunsa sun tafi saboda tsufa.

  21. Amma Ubangiji ya ce wa Ahiya, “Matar Yerobowam tana zuwa tă tambaye ka game da ɗanta, gama yana ciwo, za ka kuwa ba ta amsa kaza da kaza. Sa’ad da ta iso za tă yi kamar wata ce dabam.”

  22. Saboda haka sa’ad da Ahiya ya ji motsin sawunta a ƙofa, sai ya ce, “Ki shigo, matar Yerobowam. Me ya sa kike yi kamar wata ce dabam? An aiko ni wurinki da labari marar daɗi.

  23. Je ki faɗa wa Yerobowam cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na tā da kai daga cikin mutane, na mai da kai shugaba a bisa mutanena Isra’ila.

  24. “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus.

  25. Karnuka za su ci waɗanda suka mutu na Yerobowam a cikin birni, kuma tsuntsayen sararin sama za su cinye waɗanda suka mutu a jeji. Ni Ubangiji na faɗa!’