Skip to content

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 1:1kusan 1015 K.H.

    Sa’ad da Sarki Dawuda ya tsufa ya kuma ƙara shekaru, ba ya iya jin ɗumi ko an rufe shi da abin rufuwa.

  2. 1 Sarakuna 1:2kusan 1015 K.H.

    Saboda haka bayinsa suka ce masa, “Bari mu nemi wata budurwa wadda za tă yi wa ranka yă daɗe, sarki hidima, tă kuma kula da shi. Za tă dinga kwanta kusa da ranka yă daɗe, yă ji ɗumi.”

  3. 1 Sarakuna 1:3kusan 1015 K.H.

    Suka nemi kyakkyawar yarinya cikin fāɗin Isra’ila, sai suka sami Abishag, mutuniyar Shunam, suka kawo ta wa sarki.

  4. 1 Sarakuna 1:4kusan 1015 K.H.

    Yarinyar kuwa kyakkyawa ce ƙwarai; ta kuwa lura da sarki, ta kuma yi masa hidima, amma sarki bai yi jima’i da ita ba.

  5. 1 Sarakuna 1:5kusan 1015 K.H.

    Adoniya, wanda mahaifiyarsa ce Haggit, ya fito ya ce, “Zan zama sarki.” Saboda haka ya nemi kekunan yaƙi, ya kuma shirya dawakai, tare da mutane hamsin da za su sha gabansa.

  6. 1 Sarakuna 1:6kusan 1015 K.H.

    (A duk rayuwarsa mahaifinsa bai taɓa tsawata masa yă ce, “Me ya sa kake yin haka ba?” Shi kuwa mai kyan gani ne ƙwarai, shi ne aka haifa bayan Absalom.)

  7. 1 Sarakuna 1:7kusan 1015 K.H.

    Adoniya ya haɗa baƙi da Yowab ɗan Zeruhiya da kuma Abiyatar firist, suka kuma ba shi goyon baya.

  8. 1 Sarakuna 1:8kusan 1015 K.H.

    Amma Zadok firist, Benahiya ɗan Yehohiyada, annabi Natan, Shimeyi, Reyi da kuma matsara na musamman na Dawuda ba su bi Adoniya ba.

  9. 1 Sarakuna 1:9kusan 1015 K.H.

    Wata rana Adoniya ya tafi Dutsen Zohelet kusa da En Rogel, inda ya yi hadayar tumaki, da shanun noma, da shanun da ake kiwo a gida. Ya kuma gayyaci ’yan’uwansa, wato, sauran ’ya’yan Sarki Dawuda, tare da dukan dattawan sarki da suka fito daga Yahuda,

  10. 1 Sarakuna 1:10kusan 1015 K.H.

    amma bai gayyaci annabi Natan, ko Benahiya, ko wani daga matsara na musamman, ko kuwa ɗan’uwansa Solomon ba.

  11. 1 Sarakuna 1:11kusan 1015 K.H.

    Sai Natan ya ce wa Batsheba, mahaifiyar Solomon, “Ki san cewa Adoniya, ɗan Haggit, ya zama sarki ba tare da sanin ranka yă daɗe, sarkinmu Dawuda ba?

  12. 1 Sarakuna 1:12kusan 1015 K.H.

    Yanzu bari in ba ki shawara yadda za ki cece ranki da kuma ran ɗanki Solomon.

  13. 1 Sarakuna 1:13kusan 1015 K.H.

    Ki shiga wurin Sarki Dawuda ki ce masa, ‘Ranka yă daɗe sarki, ba ka rantse mini ni baiwarka cewa, “Tabbatacce Solomon ɗanka ne zai zama sarki bayana, yă kuma zauna a kujerar sarautar ba”? To, me ya sa Adoniya ya zama sarki?’

  14. 1 Sarakuna 1:14kusan 1015 K.H.

    Yayinda kike can kina magana da sarki, zan shiga in kuma tabbatar da abin da kika faɗa.”

  15. 1 Sarakuna 1:15kusan 1015 K.H.

    Saboda haka Batsheba ta je don tă ga sarki. A yanzu dai sarki ya tsufa, yana nan kuma a cikin ɗakinsa, inda Abishag mutuniya Shunam take masa hidima.

  16. 1 Sarakuna 1:16kusan 1015 K.H.

    Batsheba ta rusuna ta kuma durƙusa a gaban sarki. Sai sarki ya tambaye ta ya ce, “Me kike so?”

  17. 1 Sarakuna 1:17kusan 1015 K.H.

    Ta ce masa, “Ranka yă daɗe, kai kanka ka rantse mini ni baiwarka da sunan Ubangiji Allahnka cewa, ‘Solomon ɗanka zai zama sarki bayana, zai kuma zauna a kujerar sarautata.’

  18. 1 Sarakuna 1:18kusan 1015 K.H.

    Amma yanzu Adoniya ya zama sarki, kai kuwa ranka yă daɗe sarki, ba ka san wani abu game da shi ba.

  19. 1 Sarakuna 1:19kusan 1015 K.H.

    Ya miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa, ya kuma gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da Abiyatar firist, da Yowab shugaban mayaƙa, amma bai gayyaci Solomon bawanka ba.

  20. 1 Sarakuna 1:20kusan 1015 K.H.

    Ranka yă daɗe sarki, idanun dukan Isra’ila suna a kanka, domin su san wa zai zauna a kujerar ranka yă daɗe sarkina, a bayanka.

  21. 1 Sarakuna 1:21kusan 1015 K.H.

    In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.”

  22. 1 Sarakuna 1:22kusan 1015 K.H.

    Yayinda take cikin magana tare da sarki, sai annabi Natan ya iso.

  23. 1 Sarakuna 1:23kusan 1015 K.H.

    Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  24. 1 Sarakuna 1:24kusan 1015 K.H.

    Natan ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki, ko ka furta cewa Adoniya ne zai zama sarki a bayanka, yă kuma zauna a kujerar sarautarka?

  25. 1 Sarakuna 1:25kusan 1015 K.H.

    Yau ya gangara, ya kuma miƙa hadayun shanu, da shanun da ake kiwo a gida, da tumaki masu yawa. Ya gayyaci dukan ’ya’yan sarki maza, da shugaban mayaƙa, da kuma Abiyatar firist. A yanzu haka suna ci, suna sha, tare da shi, suna cewa, ‘Ran Sarki Adoniya yă daɗe!’