Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Public Prayer

128 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka.

  2. Sai Yoshuwa ya yaga tufafinsa ya fāɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, yana can har yamma. Dattawan Isra’ila ma suka yi haka, suka zuba toka a kawunansu.

  3. Yoshuwa kuma ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, me ya sa ka sa mutanen nan suka ƙetare Urdun don ka bari mu shiga hannun Amoriyawa su hallaka mu? Kila da mun haƙura mun zauna a ɗaya gefen Urdun da ya fi mana!

  4. Ya Ubangiji me zan ce, yanzu da abokan gāban Isra’ilawa suka ci ƙarfinsu?

  5. Yanzu Kan’aniyawa da sauran jama’a za su ji, za su zo su kewaye mu su share sunanmu daga duniya. To, yanzu me za ka yi don girman sunanka?”

  6. Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin.

  7. Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.

  8. Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.

  9. Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.

  10. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.

  11. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.

  12. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.

  13. Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka.

  14. Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.

  15. Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”

  16. Sa’an nan Solomon ya ce, “Ubangiji ya faɗa cewa zai zauna cikin duhun girgije;

  17. na gina ƙasaitaccen haikali dominka, wuri domin ka zauna har abada.”

  18. Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su.

  19. Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,

  20. ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.

  21. Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’

  22. “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  23. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.

  24. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’

  25. “Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.