Skip to content

Egypt

561 verses · 4 known names

An kuma san shi da: Egyptian, Egyptians, Egyptian's

30.1000, 31.3300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Egypt

Tace bisa littafi
  1. To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani.

  2. Yayinda yana gab da shiga Masar, sai ya ce wa matarsa Saira, “Na sani ke kyakkyawar mace ce.

  3. Sa’ad da Masarawa suka ganki, za su ce, ‘Wannan matarsa ce.’ Za su kuwa kashe ni, su bar ki da rai.

  4. Sa’ad da Abram ya isa Masar, Masarawa suka ga cewa Saira kyakkyawa mace ce ƙwarai.

  5. Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot.

  6. Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)

  7. A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan,

  8. Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.

  9. Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran ’yan’uwansu.

  10. Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka.

  11. Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.

  12. Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.

  13. Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.

  14. To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.

  15. Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji.

  16. Bayan ɗan lokaci, sai mai riƙon kwaf da mai tuyan sarkin Masar suka yi wa maigidansu, sarkin Masar laifi.

  17. sai kowanne a cikin mutum biyun nan, mai riƙon kwaf da mai tuya na sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, suka yi mafarki a dare ɗaya, kuma kowane mafarki ya kasance da fassara irin tasa.

  18. Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu.

  19. Bayansu kuma, sai ga waɗansu shanu bakwai suka fito ƙanjamammu, munana, ramammu. Ban taɓa ganin irin munanan shanu haka a cikin dukan ƙasar Masar ba.

  20. Shekaru bakwai na yalwar abinci suna zuwa a dukan ƙasar Masar,

  21. amma shekaru bakwai na yunwa za su biyo bayansu. Tsananin yunwar za tă sa a manta da dukan isashen abincin da aka samu a ƙasar Masar, yunwa kuwa za tă rufe dukan ƙasar.

  22. “Yanzu fa, bari Fir’auna yă nemi mutum mai basira da kuma hikima, yă sa shi yă shugabanci ƙasar Masar.

  23. Bari Fir’auna yă naɗa komishinoni a kan ƙasar don su karɓi kashi ɗaya bisa biyar na girbin Masar a lokacin shekaru bakwai na yalwar abinci.

  24. Ya kamata a adana abincin nan don ƙasar, kāriya shekaru bakwai na yunwa, domin a yi amfani da shi a lokacin shekarun yunwan da za su zo wa Masar, saboda kada ƙasar ta lalace da yunwa.”

  25. Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.”