- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Select Readings
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sai Yahuda ya haura zuwa wurinsa ya ce, “Ranka yă daɗe, roƙo nake, bari bawanka yă yi magana da ranka yă daɗe. Kada ka yi fushi da bawanka, ko da yake daidai kake da Fir’auna kansa.
Ranka yă daɗe ya tambayi bayinka ya ce, ‘Kuna da mahaifi ko ɗan’uwa?’
Muka kuwa amsa, ‘Muna da mahaifi tsoho, akwai kuma ɗa matashi, wanda aka haifa masa cikin tsufarsa. Ɗan’uwansa ya rasu, shi ne kuwa ɗa kaɗai na mahaifiyarsa da ya rage, mahaifinsa kuwa yana ƙaunarsa.’
“Sai ka ce wa bayinka, ‘Ku kawo mini shi don in gan shi da kaina.’
Muka kuwa ce wa ranka yă daɗe, ‘Saurayin ba zai iya barin mahaifinsa ba, gama in ya bar shi, mahaifinsa zai mutu.’
Amma ka faɗa wa bayinka, ‘Sai kun kawo ƙaramin ɗan’uwanku tare da ku, in ba haka ba, ba za ku sāke ganin fuskata ba.’
Sa’ad da muka koma wurin bawanka mahaifinmu, sai muka faɗa masa abin da ranka yă daɗe ya ce.
“Sai mahaifinmu ya ce, ‘Ku koma ku sayo ƙarin abinci.’
Amma muka ce, ‘Ba za mu iya gangarawa ba, sai in ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare da mu. Ba za mu iya ganin fuskar mutumin ba, sai ƙaramin ɗan’uwanmu yana tare mu.’
“Bawanka mahaifinmu ya ce mana, ‘Kun san cewa matata ta haifa mini ’ya’ya biyu maza.
Ɗayansu ya tafi daga gare ni, na kuwa ce, “Tabbatacce an yayyage shi kaca-kaca.” Ban kuwa gan shi ba tuntuni.
In kun ɗauki wannan daga wurina shi ma wani abu ya same shi, za ku kawo furfura kaina zuwa kabari cikin baƙin ciki.’
“Saboda haka yanzu, in saurayin ba ya nan tare da mu sa’ad da na koma ga bawanka mahaifina, in kuma mahaifina, wanda ransa yana daure kurkusa da ran saurayin,
ya ga cewa saurayin ba ya nan, zai mutu. Bayinka za su sa bawanka, mahaifinmu, yă mutu cikin baƙin ciki, da tsufansa.
Gama ni baranka na ɗauki lamunin saurayin a wurin mahaifinsa da cewa, ‘In ban komo maka da shi ba, sai alhakinsa yă zauna a kaina a gaban mahaifina, dukan raina!’
“To, yanzu, ina roƙonka bari bawanka yă zauna a nan a matsayin bawanka, ranka yă daɗe a maimakon saurayin, a kuma bar saurayin yă koma da ’yan’uwansa.
Yaya zan koma ga mahaifina, in saurayin ba ya tare da ni? A’a! Kada ka bari in ga baƙin cikin da zai auko wa mahaifina.”
Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga ’yan’uwansa.
Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.
Yusuf kuwa ya ce wa ’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma ’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.
Sa’an nan Yusuf ya ce wa ’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!
Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.
Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.
“Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar.