Skip to content

Zion

139 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Sion

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Zion

Tace bisa littafi
  1. Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.

  2. Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.

  3. Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona ta rena ka tana kuma yin maka ba’a. Diyar Urushalima ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.

  4. suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka, Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, Birnin Dawuda.

  5. Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.

  6. “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”

  7. Rera yabai ga Ubangiji, wanda yake zaune a kursiyi a Sihiyona; yi shela a cikin al’ummai abin da ya aikata.

  8. don in furta yabanka cikin ƙofofin ’Yar Sihiyona a can kuwa in yi farin ciki cikin cetonka.

  9. Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

  10. Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.

  11. Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta,

  12. Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa.

  13. Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.

  14. Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

  15. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu

  16. gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,

  17. Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.

  18. Suna ta ƙara ƙarfi, har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.

  19. Ubangiji yana ƙaunar ƙofofin Sihiyona fiye da dukan wuraren zaman Yaƙub.

  20. Tabbatacce, game da Sihiyona za a ce, “Wannan da wancan an haifa a cikinta, Mafi Ɗaukaka kansa zai kafa ta.”

  21. Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.

  22. Ubangiji mai girma yana a Sihiyona; an ɗaukaka shi a bisa dukan al’ummai.

  23. Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo.

  24. Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.

  25. Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima