Tsallake zuwa abun ciki

Zion

139 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Sion

31.7700, 35.2300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Zion

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

  2. Waƙar haurawa. Sa’ad da Ubangiji ya dawo da kamammu zuwa Sihiyona, mun kasance kamar mutanen da suka yi mafarki.

  3. Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,

  4. Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.

  5. Gama Ubangiji ya zaɓi Sihiyona, ya so ta zama mazauninsa,

  6. Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.

  7. Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.

  8. Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona, gare shi wanda yake zama a Urushalima. Yabi Ubangiji.

  9. A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona.

  10. gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!”

  11. Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.

  12. Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.

  13. Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

  14. Fito, ku ’yan matan Sihiyona, ku ga Sarki Solomon yana saye da rawani, rawanin da mahaifiyarsa ta naɗa masa, a ranar aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.

  15. An bar diyar Sihiyona kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, kamar bukka a gonar kabewa, kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.

  16. Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya.

  17. Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima.

  18. Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.

  19. Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”

  20. Waɗanda suka rage a Sihiyona, waɗanda suka rage a Urushalima, za a ce da su masu tsarki, wato, dukan waɗanda aka rubuta a cikin masu rai a Urushalima.

  21. Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta.

  22. Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ya mutanena masu zama a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriyawa, waɗanda suka dūke ku da sanda suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.

  23. A wannan rana za su dakata a Nob; za su jijjiga ƙarfinsu a dutsen Diyar Sihiyona, a tudun Urushalima.

  24. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

  25. Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”