- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1010–970 BC
The Reign of David
David unites the tribes, conquers Jerusalem, and establishes Israel's golden age—even through deep personal failure.
Ayoyi daga wannan lokacin
- 2 Sama’ila 1:1kusan 1053 K.H.
Bayan mutuwar Shawulu, Dawuda ya dawo daga karkashe Amalekawa. Sai ya zauna a Ziklag kwana biyu.
- 2 Sama’ila 1:2kusan 1053 K.H.
A rana ta uku sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Shawulu da yagaggen riga da ƙura a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi a ƙasa don yă nuna bangirma.
- 2 Sama’ila 1:3kusan 1053 K.H.
Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Daga ina ka fito?” Ya amsa ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra’ila.”
- 2 Sama’ila 1:4kusan 1053 K.H.
Dawuda ya ce, “Gaya mini, me ya faru?” Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga yaƙi, aka kuma karkashe yawancin mutane. Shawulu da ɗansa Yonatan ma sun mutu.”
- 2 Sama’ila 1:5kusan 1053 K.H.
Sai Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Yaya ka san cewa Shawulu da ɗansa Yonatan sun mutu?”
- 2 Sama’ila 1:6kusan 1053 K.H.
Saurayin ya ce, “Ina kan dutsen Gilbowa a lokacin sai na ga Shawulu jingine a māshinsa. Kekunan yaƙi da mahayansu suna matsowa kusa da shi.
- 2 Sama’ila 1:7kusan 1053 K.H.
Da ya juya ya gan ni sai ya kira ni, na kuwa ce masa, ‘Ga ni?’
- 2 Sama’ila 1:8kusan 1053 K.H.
“Ya tambaye ni ya ce, ‘Wane ne kai?’ “Na ce, ‘Ni mutumin Amalek ne.’
- 2 Sama’ila 1:9kusan 1053 K.H.
“Sai ya ce mini, ‘Matso kusa ka kashe ni! Ina cikin azabar mutuwa, sai dai har yanzu ina da rai.’
- 2 Sama’ila 1:10kusan 1053 K.H.
“Saboda haka na matso kusa da shi na kashe shi, domin na san cewa ba zai yi rai ba, da yake ya riga ya fāɗi. Sai na cire rawanin da yake kansa, na kuma cire warwaron hannunsa, na kuwa kawo maka su duka, ranka yă daɗe!”
- 2 Sama’ila 1:11kusan 1053 K.H.
Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka yayyage rigunarsu.
- 2 Sama’ila 1:12kusan 1053 K.H.
Suka yi makoki, da kuka, da azumi har yamma saboda Shawulu da ɗansa Yonatan, da saboda sojojin Ubangiji, da kuma gidan Isra’ila, gama an karkashe su a yaƙi.
- 2 Sama’ila 1:13kusan 1053 K.H.
Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni ɗan wani baƙo ne, mutumin Amalek.”
- 2 Sama’ila 1:14kusan 1053 K.H.
Dawuda ya ce masa, “Yaya ba ka ji tsoro ɗaga hannu ka hallaka shafaffe na Ubangiji ba?”
- 2 Sama’ila 1:15kusan 1053 K.H.
Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin mutanensa ya ce, “Je ka kashe shi!” Haka kuwa ya buge shi, ya kuwa mutu.
- 2 Sama’ila 1:16kusan 1053 K.H.
Gama Dawuda ya riga ya ce masa, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe shafaffe na Ubangiji.’ ”
- 2 Sama’ila 1:17kusan 1053 K.H.
Dawuda ya rera wannan makoki saboda Shawulu da ɗansa Yonatan.
- 2 Sama’ila 1:18kusan 1053 K.H.
Ya umarta a koya wa mutanen Yahuda wannan waƙa mai suna Makokin Baka (tana a rubuce a Littafin Yashar),
- 2 Sama’ila 1:19kusan 1053 K.H.
“Ya Isra’ila, an kashe darajarki a kan tuddanki. Ga shi, jarumawa sun fāɗi!
- 2 Sama’ila 1:20kusan 1053 K.H.
“Kada a faɗe shi a Gat, kada a yi shelarsa a titunan Ashkelon, don kada ’yan matan Filistiyawa su yi murna don kada ’yan matan marasa kaciya su yi farin ciki.
- 2 Sama’ila 1:21kusan 1053 K.H.
“Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku, balle gonakin da suke ba da hatsin hadaya su ƙara bayarwa. Gama a can ne garkuwoyin manyan sojoji suka kwanta, suka kwanta a wulaƙance. Garkuwar Shawulu kuwa, ba za a ƙara shafa mata mai ba.
- 2 Sama’ila 1:22kusan 1053 K.H.
“Daga jinin waɗanda aka kashe, daga tsokar naman jarumi, bakan Yonatan bai juye baya ba, takobin Shawulu bai komo ba tare da gamsuwa ba.
- 2 Sama’ila 1:23kusan 1053 K.H.
Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.
- 2 Sama’ila 1:24kusan 1053 K.H.
“Ya ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka saboda Shawulu, wanda ya suturta ku da jajjayen kayan ado, wanda ya yi wa rigunarku ado da zinariya.
- 2 Sama’ila 1:25kusan 1053 K.H.
“Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku.