Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abishai

43 ayoyi · 11 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

  2. Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.

  3. Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”

  4. Amma Yowab da Abishai suka fafari Abner, kuma da rana tana fāɗuwa sai suka iso tudun Amma, kusa da Giya, a hanyar zuwa jejin Gibeyon.

  5. (Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)

  6. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa.

  7. Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.

  8. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”

  9. Dawuda ya sa rundunoni kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Yowab, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Abishai, ɗan’uwan Yowab ɗan Zeruhiya, kashi ɗaya bisa uku a ƙarƙashin Ittai mutumin Gat. Sai sarki ya ce wa rundunonin, “Tabbatacce zan tafi tare da ku.”

  10. Sarki ya umarci Yowab, Abishai, da Ittai, ya ce musu, “Ku yi mini hankali da saurayin nan Absalom.” Dukan mutane kuwa suka ji yadda sarki yake ba wa kowane komanda umarni.

  11. Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce, “Bai kamata a kashe Shimeyi saboda wannan ba? Ya la’anci shafaffe na Ubangiji.”

  12. Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!”

  13. Saboda haka dukan mutane Isra’ila suka bar Dawuda don su bi Sheba ɗan Bikri. Amma mutanen Yahuda suka kasance a wurin sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.

  14. Da Dawuda ya komo fadarsa a Urushalima, sai ya ɗauko ƙwarƙwaran goma nan da ya bari su lura da fada, ya keɓe su a wani gida inda za a yi tsaronsu. Ya tanada musu, amma bai kwana da su ba. Aka sa su a keɓe har iyakar rayuwarsu, suka yi zama kamar gwauraye.

  15. Sa’an nan sarki ya ce wa Amasa, “Ka tattaro mutanen Yahuda su zo wurina cikin kwana uku, kai kuwa ka kasance a can kai kanka.”

  16. Amma da Amasa ya tafi kiran mutanen Yahuda, ya ɗauki lokaci fiye da lokacin da sarki ya ba shi.

  17. Dawuda ya ce wa Abishai, “Ina gani Sheba ɗan Bikri zai ba mu wuya fiye da Absalom. Ka ɗauki mutanen maigidanka ka fafare shi, don kada yă sami garuruwa masu katanga yă tsere mana.”

  18. Saboda haka mutanen Yowab da Keretawa da Feletiyawa da dukan jarumawa suka fita a ƙarƙashin Abishai. Suka fita daga Urushalima don su fafari Sheba ɗan Bikri.

  19. Yayinda suke a babban dutse a Gibeyon, Amasa ya zo don yă tarye su. Yowab kuwa yana sanye da doguwar rigar soja, a ɗamarar da ya sha kuwa akwai wuƙa a cikin kube. Da ya zo gaba sai wuƙar ta zāre daga kube ta fāɗi.

  20. Yowab ya ce wa Amasa, “Yaya kake, ɗan’uwana?” Sai Yowab ya kama gemun Amasa da hannun dama don yă yi masa sumba.

  21. Amasa kuwa bai lura da wuƙar da take hannun Yowab ba, Yowab kuwa ya soke shi da wuƙar a ciki, hanjinsa suka zube ƙasa. Ba tare da ƙarin suƙa ba, Amasa ya mutu. Sa’an nan Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka fafari Sheba ɗan Bikri.

  22. Ɗaya daga cikin mutanen Yowab ya tsaya kusa da Amasa ya ce, “Duk mai son Yowab, kuma duk mai son Dawuda, yă bi Yowab!”

  23. Amasa kuwa yana kwance cikin tafkin jininsa a kan hanya, sai mutumin ya ga dukan sojoji suka zo suka tsaya cik a can. Da ya gane cewa duk wanda ya haura zuwa wurin Amasa sai ya tsaya, sai ya ja gawar Amasa daga hanyar ya kai can cikin wani fili ya rufe shi da zane.

  24. Bayan an ɗauke Amasa daga hanya, sai dukan mutane suka bi Yowab don fafaran Sheba ɗan Bikri.

  25. Sheba ya bi ta dukan kabilan Isra’ila zuwa Abel da kuma ta dukan yankin Beriyawa, waɗanda suka taru suka bi shi.