Skip to content

Bethlehem

32 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Beth-lehem

31.7000, 35.2100 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Bethlehem

Tace bisa littafi
  1. Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).

  2. Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).

  3. Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.

  4. Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.

  5. Saboda haka matan biyu suka ci gaba da tafiya sai da suka isa Betlehem. Da suka isa Betlehem, sai dukan garin ya ruɗe saboda su, matan kuwa suka ce, “Na’omi ce wannan kuwa?”

  6. Na’omi fa ta koma daga Mowab tare da Rut mutuniyar Mowab, surukarta, suka kai Betlehem a lokacin da ake fara girbin sha’ir.

  7. Sai ga Bowaz ya iso daga Betlehem ya gai da masu girbi, “Ubangiji yă kasance tare da ku!” Sai suka amsa, “Ubangiji yă albarkace ka!”

  8. Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.

  9. Sama’ila kuwa ya yi abin da Ubangiji ya umarce shi. Da ya isa Betlehem, sai dattawan garin suka tarye shi da rawar jiki, suka ce masa, “Mai duba, wannan ziyara lafiya dai ko?”

  10. Amma Dawuda yakan tafi sansanin Shawulu lokaci-lokaci yă kuma koma Betlehem don yă yi kiwon tumakin mahaifinsa.

  11. In mahaifinka bai gan ni ba, ka gaya masa cewa, ‘Dawuda ya nemi izinina domin yă hanzarta yă tafi garinsa a Betlehem saboda ana hadaya ta shekara-shekara don dukan zuriyarsa.’

  12. Yonatan ya ce, “Dawuda ya nemi izinina don yă tafi Betlehem.

  13. Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe.

  14. Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.

  15. Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”

  16. Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.

  17. Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,

  18. A lokacin Dawuda yana cikin mafaka, sojojin Filistiyawa kuma suna a Betlehem.

  19. Dawuda ya ji marmarin ruwan sha sai ya ce, “Kash, a ce wani zai sami mini ruwan sha daga rijiya kusa da ƙofar Betlehem mana!”

  20. Sai Ukun suka kutsa kai cikin sansanin Filistiyawa, suka ja ruwa daga rijiyar da take kusa da ƙofar Betlehem suka ɗauko shi suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi yă sha; a maimako, sai ya zubar da shi a gaban Ubangiji.

  21. Jarumawan nan su ne, Asahel ɗan’uwan Yowab, Elhanan ɗan Dodo daga Betlehem,

  22. Betlehem, Etam, Tekowa,

  23. Mutanen Betlehem 123

  24. Mutanen Betlehem da na Netofa 188

  25. Sai suka ci gaba, suka dakata a Gerut Kimham kusa da Betlehem a kan hanyarsu zuwa Masar