Skip to content

Joab

120 ayoyi · 3 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Joab

Tace bisa littafi
  1. Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

  2. Yowab wanda ake ce mamarsa Zeruhiya tare da waɗansu mutanen Dawuda suka fito suka haɗu da su tafkin Gibeyon, Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe.

  3. Sa’an nan Abner ya ce wa Yowab, “Bari mu bar waɗansu samari su tashi su yi faɗa hannu da hannu a gabanmu.” Yowab ya ce, “To, su tashi.”

  4. ’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa.

  5. Abner ya sāke gargaɗe shi ya ce, “Ka bar fafarata! Yaya zan kashe ka? Yaya zan yin ido biyu da ɗan’uwanka Yowab?”

  6. Amma Yowab da Abishai suka fafari Abner, kuma da rana tana fāɗuwa sai suka iso tudun Amma, kusa da Giya, a hanyar zuwa jejin Gibeyon.

  7. Sai Abner ya kira Yowab ya ce, har abada ne māshi zai yi ta hallakarwa? Ba ka sani cewa ƙarshen zai zama da ɗaci ba. Sai yaushe za ka umarci mutanenka su daina fafaran ’yan’uwansu?

  8. Yowab ya ce, “Muddin Allah yana a raye, da ba a ce ka yi magana ba, da mutanen za su ci gaba da fafaran ’yan’uwansu har gari yă waye.”

  9. Sai Yowab ya busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka tsaya; suka daina fafaran Isra’ila. Nan take faɗan ya tsaya.

  10. Da Yowab ya dawo daga fafaran Abner, sai ya tattara dukan mutanensa. Ban da Asahel, sai ya gane an rasa mutum goma sha tara na Dawuda.

  11. Suka ɗauki gawar Asahel suka binne a kabarin mahaifinsa a Betlehem. Sa’an nan Yowab da mutanensa suka bi dare har suka iso Hebron da safe.

  12. Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya.

  13. Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya.

  14. Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi!

  15. Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba.

  16. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.

  17. Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”

  18. (Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)

  19. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.

  20. Yowab ɗan Zeruhiya ya zama shugaban sojoji; Yehoshafat ɗan Ahilud kuwa shi ne marubucin tarihi;

  21. Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.

  22. Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa.

  23. Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa.

  24. Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.

  25. Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.