Tsallake zuwa abun ciki

Joab

120 ayoyi · 3 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Joab

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Dawuda ya aika saƙo wa Yowab ya ce, “Ka aiko mini da Uriya mutumin Hitti.” Yowab kuwa ya aika da shi wajen Dawuda.

  2. Da Uriya ya zo wurinsa, sai Dawuda ya tambaye shi lafiyar Yowab da sojojin, da kuma yaya yaƙin yake tafiya.

  3. Sai Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin Alkawari, da Isra’ila, da Yahuda suna zama cikin tentuna, kuma maigidana Yowab da mutanen ranka yă daɗe suna a sansani a fili. Yaya zan je gidana in ci in sha in kuma kwana da matata? Muddin kana a raye, ba zan yi irin wannan abu ba!”

  4. Da safe Dawuda ya rubuta wa Yowab wasiƙa ya ba wa Uriya.

  5. Saboda haka yayinda Yowab ya kai yaƙi kusa da birnin, sai tura Uriya a inda ya sani akwai jarumawan Ammon na gaske.

  6. Sa’ad da mutanen garin suka fito suka yaƙi Yowab, sai waɗansu mutane daga sojojin Dawuda suka mutu; Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.

  7. Yowab ya aika wa Dawuda cikakken labari batun yaƙin.

  8. Manzon ya tashi ya tafi, da ya iso kuwa sai ya gaya wa Dawuda dukan abin da Yowab ya aike shi yă faɗa.

  9. Dawuda ya ce wa manzon, “Ka gaya wa Yowab, ‘Kada ka bar wannan yă dame ka; yadda takobi ya lamushe wannan, haka zai lamushe wancan ma. Ku ƙara matsa wa garin lamba, ku hallaka shi.’ Ka faɗa haka don ka ƙarfafa Yowab.”

  10. Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin.

  11. Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta.

  12. Yowab, ɗan Zeruhiya ya gane cewa zuriyar sarki ta koma ga Absalom.

  13. Saboda haka Yowab ya aiki wani zuwa Tekowa, ya sa a zo da wata mace mai hikima. Ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki. Ki sa rigar makoki, kada kuwa ki shafa mai. Ki yi kamar macen da ta yi kwanaki da yawa, tana makokin matattu.

  14. Sa’an nan ki je wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai Yowab ya faɗa mata duk abin da za tă faɗa.

  15. Sarki ya ce, “Anya, babu hannun Yowab a cikin dukan wannan?” Matar ta ce, “Muddin kana a raye, ranka yă daɗe sarki, ba wanda zai juya dama ko hagu daga wani abin da ranka yă daɗe sarki ya faɗa. I, bawanka Yowab ne ya umarce ni in yi wannan, shi ne kuma ya sa kalmomin nan a bakin baiwarka.

  16. Bawanka Yowab ne ya yi haka don yă daidaita al’amura. Ranka yă daɗe yana da hikima iri ta mala’ikan Allah, ya san dukan kome da yake faruwa a ƙasar.”

  17. Sarki ya ce wa Yowab, “To, da kyau, zan yi haka. Je ka, ka dawo da saurayin nan Absalom.”

  18. Yowab ya rusuna har ƙasa don bangirma, ya kuma yi wa sarki kyakkyawar fata. Yowab ya ce, “Yau, bawanka ya sani ya sami tagomashi a gare ka, ranka yă daɗe sarki, gama sarki ya ji roƙon bawansa.”

  19. Sa’an nan Yowab ya tafi Geshur ya dawo da Absalom Urushalima.

  20. Sai Absalom ya aika a kira masa Yowab don yă aike shi wurin sarki, amma Yowab ya ƙi zuwa. Saboda haka ya sāke aika sau na biyu, amma ya ƙi yă zo.

  21. Sai ya ce wa bayinsa, “Duba, gonar Yowab tana gab da tawa, kuma yana da sha’ir a can. Ku je ku sa mata wuta.” Sai bayin Absalom suka sa wa gonar wuta.

  22. Sa’an nan Yowab ya tafi gidan Absalom ya ce masa, “Me ya sa bayinka suka sa wa gonata wuta?”

  23. Absalom ya ce wa Yowab, “Kai, na aika, ‘Ka zo nan don in aike ka wurin sarki ka tambaya, “Me ya sa na dawo daga Geshur? Ai, ya fi mini a ce ina can har yanzu!” ’ Yanzu kuwa, ina so in ga sarki, kuma idan na yi wani laifi, to, yă kashe ni.”

  24. Saboda haka Yowab ya tafi wurin sarki ya gaya masa wannan. Sai sarki ya aika aka zo da Absalom, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa a gaban sarki. Sarki kuwa ya sumbaci Absalom.

  25. Absalom ya riga ya naɗa Amasa a kan sojoji a maimakon Yowab. Amasa kuwa ɗan wani mutum mai suna Itra ne, mutumin Ishmayel wanda ya auri Abigiyel, ’yar Nahash, ’yar’uwar Zeruhiya mahaifiyar Yowab.