Skip to content

Edom

80 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Idumea, Syria

30.7300, 35.6000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Edom

Tace bisa littafi
  1. Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom.

  2. Kora, Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.

  3. ’Ya’yan Reyuwel maza, Shugabannin su ne; Nahat, Zera, Shamma da Mizza. Waɗannan su ne manya da suka fito daga dangin Reyuwel a Edom; su ne jikokin Basemat matar Isuwa.

  4. Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.

  5. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,

  6. Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.

  7. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom bisa ga mazauninsu cikin ƙasar da suka zauna. Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom.

  8. Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.

  9. Musa ya aiki manzanni daga Kadesh zuwa wurin sarkin Edom cewa, “Ga abin da ɗan’uwanka Isra’ila ya ce ka san duk irin wahalolin da ya same mu.

  10. Amma Edom ya amsa ya ce, “Ba za ku bi ta nan ba; in kuka kuskura, za mu fito, mu yaƙe ku da takobi.”

  11. Sai mutanen Edom suka sāke amsa suka ce, “Ba za ku bi nan ba dai.” Sai Edom ya fito da runduna mai ƙarfi da yawa gaske a kan Isra’ila.

  12. Da yake Edom suka ƙi su bar su su ratsa yankinsu, sai Isra’ila suka juya suka janye daga gare su.

  13. A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  14. Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya;

  15. Za a ci Edom da yaƙi; za a ci Seyir, abokiyar gābanta, amma Isra’ila zai ƙara ƙarfi.

  16. Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.

  17. “ ‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,

  18. An raba wa kabilar Yahuda gādonsu ta wurin yin ƙuri’a, bisa ga iyalansu, rabon ya kai har zuwa sashen Edom, zuwa Jejin Zin can kurewar kudu.

  19. Garuruwan kabilar Yahuda da suke kudu cikin Negeb zuwa iyakar Edom su ne. Kabzeyel, Eder, Yagur,

  20. “Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir, sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom, ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo, gizagizai sun zubo da ruwa.

  21. Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.

  22. “Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.

  23. Bayan Shawulu ya hau karagar mulkin Isra’ila, ya yi yaƙi da abokan gābansu ta kowane gefe. Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, sarakunan Zoba, da kuma Filistiyawa. Duk wurin da ya juya, ya hore su.

  24. wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

  25. Ya ajiye rundunar sojoji ko’ina a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba wa Dawuda nasara a duk inda ya tafi.