Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Moabites

122 ayoyi · 56 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. ’Yar farin ta haifi ɗa, ta kuma ba shi suna Mowab, shi ne mahaifin Mowabawa a yau.

  2. Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.

  3. Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa.

  4. Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.

  5. “Mayaƙansa sun fito kamar harshen wuta suka ƙone birnin Ar na Mowab suna hallaka ’yan ƙasar tuddan Arnon.

  6. Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.

  7. “Amma mun tumɓuke su, mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon. Mun ragargaza su har zuwa Nofa wanda ya miƙe zuwa Medeba.”

  8. Sai Mowab ya firgita ƙwarai saboda yawan mutanen. Tsoron Isra’ilawa ya kama su.

  9. Sai Mowabawa suka ce wa dattawan Midiyawa, “Wannan taron zai lashe duk abin da ya kewaye mu kamar yadda saniya takan lashe ciyawa a fili.” Saboda haka Balak ɗan Ziffor, wanda yake sarkin Mowab a lokacin,

  10. Sai Bala’am ya furta abin da Allah ya faɗa masa ya ce, “Balak ya kawo ni daga Aram, sarkin Mowab ya kawo ni daga gabashin duwatsu. Ya ce, ‘Zo, ka la’anta mini Yaƙub; zo, ka tsine Isra’ila.’

  11. “Na gan shi, amma ba yanzu ba; na hange shi, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga Yaƙub; sandan mulki zai fito daga Isra’ila. Zai ragargaje goshin Mowab, kawunan dukan ’ya’yan Set.

  12. Lokacin da Isra’ila suke a sansani a Shittim, sai maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa,

  13. waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada.

  14. Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.

  15. Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ku dami Mowabawa, ko ku tsokane su da yaƙi, gama ba zan ba ku wani sashe na ƙasarsu ba. Na ba da Ar ga zuriyar Lot, ta zama mallakarsu.”

  16. (Emawa, mutane ne masu ƙarfi da kuma yawa, suna kuma da tsayi kamar Anakawa, dā sun zauna a can.

  17. Kamar Anakawa, su ma an ɗauka su Refahiyawa ne, amma Mowab suna kiransu Emawa.

  18. kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.”

  19. Ba mutumin Ammon, ko mutumin Mowab, ko kuwa wani zuriyarsu da zai shiga taron jama’ar Ubangiji, har tsara ta goma.

  20. Gama ba su zo sun tarye ku da burodi da ruwa a hanyarku, sa’ad da kuka fito daga Masar ba, sai ma suka yi haya Bala’am ɗan Beyor daga Fetor a Aram-Naharayim yă furta la’ana a kanku.

  21. Kada ku yi yarjejjeniyar abuta da su, muddin kuna da rai.

  22. Lokacin da Balak ɗan Ziffor, sarkin Mowab, ya yi shiri yă yaƙi Isra’ila, ya aiki Bala’am ɗan Beyor don yă la’anta ku.

  23. yana cewa, “Ga abin da Yefta yake faɗi, Isra’ila ba tă ƙwace ƙasar Mowab ko ta Ammonawa ba.

  24. Sa’an nan Isra’ila ta aiki jakadu zuwa ga sarkin Edom cewa, ‘Ka ba mu izini mu ratsa ƙasarka,’ amma sarkin Edom bai saurara ba. Suka kuma aika wa sarkin Mowab, shi ma ya ƙi. Saboda haka Isra’ila ta zauna a Kadesh.

  25. “Daga can suka ci gaba ta hamada, suka zaga ƙasashen Edom da Mowab, suka wuce ta gabashin ƙasar Mowab, sa’an nan suka yi sansani a ɗaya gefen Arnon. Ba su shiga yankin Mowab ba, gama Arnon ce iyakarta.