Skip to content

Chemosh

8 ayoyi

Ayoyin da suka ambaci Chemosh

  1. Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.

  2. Ba za ka karɓi abin da allahnka Kemosh ya ba ka ba? Haka mu ma, duk abin da Ubangiji Allahnmu ya riga ya ba mu, za mu mallake shi.

  3. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.

  4. Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.

  5. Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon.

  6. Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku, ku ma za a kwashe ku bayi, Kemosh zai tafi bauta, tare da firistocinsa da fadawansa.

  7. Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh, yadda gidan Isra’ila ya ji kunya sa’ad da suka dogara ga Betel.

  8. Kaitonki, ya Mowab! Mutanen Kemosh sun hallaka; an kai ’ya’yanki maza daurin talala ’ya’yanki mata zaman bauta.