Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Mountains

136 ayoyi · 82 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ruwa ya ƙaru ƙwarai a duniya, ya kuma rufe dukan duwatsu masu tsawo a ƙarƙashin sammai.

  2. Ruwan ya taso ya rufe duwatsu, zurfin ruwa daga duwatsun zuwa inda jirgin yake ya fi ƙafa ashirin.

  3. A rana ta goma sha bakwai ga watan bakwai, jirgin ya sauka a duwatsun Ararat.

  4. da Horiyawa a ƙasar tudun Seyir har zuwa El Faran kusa da hamada.

  5. Kwarin Siddim kuwa ya cika da ramummukan kwalta, sa’ad da sarakunan Sodom da Gomorra suka gudu kuwa, waɗansu mutane suka fāɗa cikin ramummukan kwaltan, sauran kuwa suka gudu zuwa tuddai.

  6. Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”

  7. Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.”

  8. Saboda haka ya gudu da dukan abin da ya mallaka, ya ƙetare Kogi, ya nufi yankin tuddan Gileyad.

  9. Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma.

  10. Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.

  11. Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin ’yan’uwansa.

  12. Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah.

  13. Sai Allah ya ce, “Zan kasance da tare kai. Wannan kuwa za tă zama alama a gare ka cewa Ni na aike ka. Bayan ka fitar da mutanen daga Masar, za ku yi sujada ga Allah a kan dutsen nan.”

  14. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi.

  15. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”

  16. Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.

  17. Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.

  18. Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor.

  19. daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada.

  20. “Atarot, Dibon, Yazer, Nimra, Heshbon, Eleyale, Sebam, Nebo da Beyon,

  21. Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.

  22. Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.

  23. “ ‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,

  24. za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,

  25. Ina roƙonka, bari in ƙetare in ga ƙasa mai kyau ɗin nan a ƙetaren Urdun, wannan ƙasar mai kyau ta tuddai, da kuma Lebanon.”