Skip to content

Carmel

22 verses · 3 known names

An kuma san shi da: Carmelite, Carmelitess

31.4300, 35.1300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Carmel

  1. sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya

  2. Mawon, Karmel, Zif, Yutta

  3. Allammelek, Amad da Mishal. A arewanci kuma iyakar ta taɓa Karmel da Shihor Libnat.

  4. Kashegari da sassafe sai Sama’ila ya tashi ya tafi domin yă sadu da Shawulu, amma aka gaya masa cewa Shawulu ya tafi Karmel. A can ya yi wa kansa abin tunawa don yă girmama kansa, daga can kuma ya juya ya gangara zuwa Gilgal.

  5. A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.

  6. Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,

  7. “Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata.

  8. Bayin Dawuda suka tafi Karmel suka ce wa Abigiyel, “Dawuda ya aike mu gare ki, mu zo mu ɗauke ki ki zama matarsa.”

  9. Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel.

  10. An kama matan Dawuda, wato, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal mutumin Karmel wanda ya rasu.

  11. Saboda haka sai Dawuda ya tafi can tare da matansa biyu, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel.

  12. na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;

  13. Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi,

  14. Hezro mutumin Karmel, Na’arai ɗan Ezbai,

  15. Kanki ya yi miki rawani kamar Dutsen Karmel. Gashinki ya yi kamar shunayya; yakan ɗauke hankalin sarki.

  16. Ƙasa tana kuka an kuma gudu an bar ta, Lebanon ta sha kunya ta kuma yanƙwane; Sharon ta zama kamar Araba, Bashan da Karmel sun kakkaɓe ganyayensu.

  17. zai buɗu ya hudo; zai yi farin ciki mai girma ya kuma yi sowa don farin ciki. Za a maido wa Lebanon da darajarta, darajar Karmel da Sharon; za su ga ɗaukakar Ubangiji, darajar Allahnmu.

  18. “Muddin ina raye,” in ji Sarki, wanda sunansa ne Ubangiji Maɗaukaki, “wani zai ɓullo wanda yake kamar Tabor a cikin duwatsu, kamar Karmel kusa da teku.

  19. Amma zan komo da Isra’ila zuwa wurin kiwonsa zai kuwa yi kiwo a Karmel da Bashan; zai ƙosar da marmarinsa a tuddan Efraim da Gileyad.

  20. Ya ce, “Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona ya kuma yi tsawa daga Urushalima; wuraren kiwo duk sun bushe, dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”

  21. Ko da sun ɓuya a bisa Karmel, a can zan farauce su in cafko. Ko da sun ɓuya can ƙarƙashin teku, a can zan umarci maciji yă sare su.

  22. Yakan tsawata wa teku yă kuma busar da shi; yakan sa dukan koguna su kafe. Bashan da Karmel sun yi yaushi tohon Lebanon kuma ya koɗe.