- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nabal
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.
Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne.
Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.
Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,
su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi!
“Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata.
Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”
Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.
Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.
Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”
Mutanen Dawuda suka juya suka koma. Da suka iso sai suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce.
Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu.
Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.
Waɗannan mutane kuwa sun yi mana kirki ƙwarai, ba su ba mu wata wahala ba. Babu abu guda da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su.
Dare da rana sun zama mana katanga kewaya da mu, a duk tsawon lokacin da muke kiwon tumakinmu kusa da su.
Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.”
Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.
Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba.
Da tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa suna gangarowa zuwa wajen da take. Sai ta tafi, ta sadu da su.
Bai daɗe ba da Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abinsa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.
Bari Allah yă yi duk abin da ya ga dama da ni in na bar ko ɗaya daga mazan da suke da tare shi, gobe da safe.”
Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa.
Ta fāɗi a ƙafafunsa ta ce, “Bari laifin yă zama nawa, ranka yă daɗe. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka ji abin da baiwarka za tă ce.
Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba.
Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal.