Skip to content

Nabal

18 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Nabal

  1. Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne.

  2. Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.

  3. Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,

  4. Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.

  5. Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.

  6. Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.

  7. Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba.

  8. Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba.

  9. Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal.

  10. Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.”

  11. Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.

  12. Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.

  13. Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu.

  14. Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.” Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa.

  15. Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel.

  16. An kama matan Dawuda, wato, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal mutumin Karmel wanda ya rasu.

  17. Saboda haka sai Dawuda ya tafi can tare da matansa biyu, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel.

  18. na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;