Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wife

171 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

  2. Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”

  3. Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  4. Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.”

  5. Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.”

  6. Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.

  7. Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”

  8. Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.

  9. Sai Rahila da Liyatu suka amsa suka ce, “Muna da wani rabo a gādon kayan mahaifinmu ne?

  10. Ba kamar baƙi ne yake ɗaukarmu ba? Ba sayar da mu kaɗai ya yi ba, har ma ya yi amfani da abin da aka biya saboda mu.

  11. Tabbatacce dukan dukiyar da Allah ya kwashe daga mahaifinmu ya zama namu da ’ya’yanmu. Saboda haka ka yi duk abin da Allah ya faɗa maka.”

  12. Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”

  13. Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata ’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai ’ya’yansa maza sun dawo gida, gama ’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo.

  14. Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.

  15. Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.

  16. Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura.

  17. Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da ’ya’yanku mata, ku kuma ku auro ’ya’yanmu mata wa kanku.

  18. Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.”

  19. Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar.

  20. Amma Ziffora ta ɗauki dutsen ƙanƙara mai ci, ta yanke loɓar ɗanta ta taɓa ƙafafun Musa da shi. Ta ce, “Tabbatacce kai angon jini ne a gare ni.”

  21. “In mutum ya sayar da ’yarsa a matsayin baiwa, ba za a ’yantar da ita kamar bawa ba.

  22. In ba tă gamshi maigida wanda ya zaɓe ta domin kansa ba, dole yă bari a fanshe ta. Ba shi da dama yă sayar da ita ga baƙi, tun da yake bai kyauta mata ba.

  23. In ya zaɓe ta domin ɗansa, dole yă ba ta duk damar da ’ya ta mace take da shi.

  24. In ya auri wata mace, ba zai hana wa baiwar abinci da sutura ba, ba kuma zai ƙi kwana da ita ba.

  25. In bai tanada mata waɗannan abubuwa uku ba, sai tă tafi ’yantacciya, babu biyan kome.