Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wife: Procured

8 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Procured

  1. Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”

  2. Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata ’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai ’ya’yansa maza sun dawo gida, gama ’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo.

  3. Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.

  4. Da ’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da ’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.

  5. Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan ’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura.

  6. Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da ’ya’yanku mata, ku kuma ku auro ’ya’yanmu mata wa kanku.

  7. Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.”

  8. Sai Yahuda ya auro wa Er mata, ɗansa na fari, sunanta Tamar.