Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wife: Relation of, to husband

13 ayoyi · 13 fannoni

Ayoyi game da Relation of, to husband

  1. Ubangiji Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

  2. Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”

  3. Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

  4. To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne.

  5. Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa.

  6. Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan.

  7. In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta.

  8. Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne.

  9. Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji.

  10. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.

  11. Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta.

  12. Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba.

  13. Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.