Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wife

171 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal.

  2. Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka.

  3. Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye.

  4. Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa.

  5. Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila,

  6. kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.”

  7. Dawuda ya ce wa Abigiyel, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau.

  8. Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana.

  9. Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.”

  10. Sa’an nan Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa daga hannunta, ya kuma ce mata, “Ki koma gida kada ki damu, na ji koke-kokenki, zan kuma biya miki bukatarki.”

  11. Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.

  12. Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.

  13. Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu.

  14. Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.” Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa.

  15. Bayin Dawuda suka tafi Karmel suka ce wa Abigiyel, “Dawuda ya aike mu gare ki, mu zo mu ɗauke ki ki zama matarsa.”

  16. Sai ta rusuna da fuskarta har ƙasa ta ce, “Ni baranyarka ce, na shirya in bauta maka in kuma wanke ƙafafun bayin shugabana.”

  17. Abigiyel ta tashi da sauri ta hau jaki, ta kuma sa ’yan mata biyar da suke mata hidima su bi ta, suka tafi tare da ’yan saƙon Dawuda. Ta kuwa zama matarsa.

  18. A rana ta bakwai, sa’ad da Sarki Zerzes, ya yi tilis da ruwan inabi, sai ya umarci bābānni bakwai waɗanda suke yin masa hidima, wato, Mehuman, Bizta, Harbona, Bigta, Abagta, Zetar da Karkas,

  19. su kawo Sarauniya Bashti a gabansa, sanye da rawanin sarautarta, don ta nuna kyanta wa mutane da kuma hakimai, gama ita kyakkyawa ce ƙwarai.

  20. Amma da masu hidima suka ba da umarnin sarki, sai Sarauniya Bashti ta ƙi zuwa. Wannan ya ɓata wa sarki rai, ya kuma yi fushi ƙwarai.

  21. Da yake, al’ada ce sarki yă nemi shawara daga sanannu a batun doka da adalci, sai ya yi magana da masu hikima waɗanda suke fahimtar lokuta

  22. suke kuma mafi kusa da sarki. Waɗannan masu hikima kuwa su ne, Karshena, Shetar, Admata, Tarshish, Meres, Marsena da kuma Memukan. Su hakimai bakwai ne na Farisa da Mediya waɗanda suke da dama ta musamman ta kaiwa ga sarki, suke kuma da matsayi mafi girma a masarautar.

  23. Ya ce, “Bisa ga doka, me za a yi wa Sarauniya Bashti? Gama ta ƙi yin biyayya da umarnin sarki Zerzes da bābānni suka kai mata?”

  24. Sai Memukan ya amsa a gaban sarki da hakimai ya ce, “Sarauniya Bashti ta yi laifi, ba ga sarki kaɗai ba, amma ga dukan hakimai ma, da kuma mutanen dukan lardunan sarki Zerzes.

  25. Domin halin Sarauniya zai zama sananne ga dukan mata, ta haka kuwa za su ƙasƙantar da mazansu su kuma ce, ‘Sarki Zerzes ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa, amma ta ƙi zuwa.’