Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wife

171 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

  2. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

  3. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.

  4. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.

  5. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.

  6. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

  7. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.

  8. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.

  9. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.

  10. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.

  11. Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya.

  12. ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,

  13. “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo, amma ke kin fi su duka.”

  14. Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe; amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.

  15. Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta, bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.

  16. Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta.

  17. Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.

  18. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma.

  19. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

  20. Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba.

  21. Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta.

  22. In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.

  23. Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta.

  24. In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren.

  25. Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.