Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wife

171 ayoyi · 13 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.

  2. Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne.

  3. “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”

  4. Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.

  5. Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

  6. Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

  7. A haka kuma, dole matansu su zama matan da suka cancanci girmamawa, ba masu gulma ba, sai dai masu sauƙinkai da kuma masu aminci a cikin kome.

  8. Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,

  9. aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.

  10. Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.

  11. Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari.

  12. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu,

  13. su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

  14. Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba

  15. sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi.

  16. Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada.

  17. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.

  18. Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya,

  19. kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.

  20. Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.

  21. Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.