Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Travellers

110 ayoyi · 39 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya bayyana ga Ibrahim kusa da manyan itatuwan Mamre yayinda yake zaune a mashigin tentinsa da tsakar rana.

  2. Da Ibrahim ya ɗaga ido, sai ya ga mutum uku suna tsaye kusa da shi. Sa’ad da ya gan su, sai ya tashi nan da nan daga mashigin tentinsa, ya tarye su, ya rusuna har ƙasa.

  3. Ya ce, “Ranka yă daɗe, in na sami tagomashi daga gare ku kada ku wuce bawanku.

  4. Bari a kawo ruwa ku wanke ƙafafunku, ku huta a ƙarƙashin wannan itace.

  5. Bari in samo muku wani abu ku ci don ku wartsake, sa’an nan ku ci gaba da tafiyarku; da yake kun biyo wurin bawanku.” Suka ce, “To, sai ka yi abin da ka ce.”

  6. Saboda haka Ibrahim ya ruga zuwa wurin Saratu a cikin tenti ya ce, “Yi sauri, ki shirya mudu uku na gari mai laushi, ki cuɗa shi, ki yi burodi.”

  7. Sa’an nan Ibrahim ya yi gudu zuwa garkensa, ya zaɓi ɗan maraƙi ya ba wa bawansa, bawansa kuma ya yi sauri ya gyara shi.

  8. Sa’an nan Ibrahim ya ɗauko dambu da madara da naman ɗan maraƙin da aka gyara, ya kawo a gabansu. Yayinda suke ci, ya tsaya a gindin itace kusa da su.

  9. Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.” Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.”

  10. Lot ya fita daga cikin gida, ya rufe ƙofar a bayansa. Ya je wurin mutanen

  11. ya ce musu, “A’a, abokaina kada ku yi wannan mummunan abu.

  12. Duba, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.”

  13. Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.

  14. Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.

  15. Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.

  16. Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.

  17. Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.

  18. Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.”

  19. Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.”

  20. Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu.

  21. Sa’an nan aka ajiye abinci a gabansa, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Sai Laban ya ce, “Faɗa mana.”

  22. Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri,

  23. Yaƙub ya bar Beyersheba ya kama hanyar Haran.

  24. Sai Laban ya ɗauki danginsa tare da shi, ya bi bayan Yaƙub har kwana bakwai, ya kuma same shi a yankin tuddan Gileyad.

  25. Me ya sa ka gudu a ɓoye ka kuma ruɗe ni? Me ya sa ba ka faɗa mini don in sallame ka da farin ciki da waƙoƙi haɗe da kiɗin ganguna da garayu ba?