Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Travellers: Generally halted at wells or streams

6 ayoyi · 39 fannoni

Ayoyi game da Generally halted at wells or streams

  1. Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.

  2. Saboda haka kyautai Yaƙub suka sha gabansa, amma shi kansa ya kwana a sansani.

  3. Bayan ya sa suka haye rafin, haka ma ya tura dukan mallakarsa zuwa hayen.

  4. Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.

  5. Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bari a bakin Kwarin Besor, sai suka taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su, sai ya gaishe su.

  6. Rijiyar Yaƙub kuwa tana can, Yesu kuwa, saboda gajiyar tafiya, sai ya zauna a bakin rijiyar. Wajen sa’a ta shida ne.