Skip to content

Succoth

10 verses

32.1900, 35.6300 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Succoth

  1. Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot.

  2. kuma a cikin kwari, Bet-Haram, Bet-Nimra, Sukkot da Zafon da kuma sauran masarautar Sihon sarkin Heshbon (gabashin Urdun, abin da ya kama har zuwa ƙarshen Tekun Kinneret).

  3. Ya ce wa mutanen Sukkot, “Ku ba wa mutanena burodi; sun gaji, har yanzu ina fafarar Zeba da Zalmunna, sarakunan Midiyawa.”

  4. Amma shugabannin Sukkot suka ce, “Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Don me za mu ba wa mayaƙanka burodi?”

  5. Daga nan ya wuce zuwa Fenuwel ya yi irin roƙon nan, amma suka amsa yadda mutanen Sukkot suka yi.

  6. Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin.

  7. Sa’an nan Gideyon ya zo ya ce wa mutanen Sukkot, “To, ga Zeba da Zalmunna, waɗanda kuka yi mini ba’a kuna cewa, ‘Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Me zai sa mu ba mutanenka da suka gaji burodi?’ ”

  8. Ya kwashe dattawan garin ya koya wa mutanen Sukkot hankali ta wurin hukunta su da ƙayayyuwan hamada.

  9. Sarki ya sa aka yi zubi a abin yin tubalin laka a filin Urdun, tsakanin Sukkot da Zaretan.

  10. Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda.