Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Molding

12 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”

  2. Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”

  3. “Kada ku yi alloli na zubi.

  4. “ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  5. Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”

  6. Ya yi ginshiƙan tagulla, kowanne tsayinsa kamu goma sha takwas, ya kuma yi guru mai kamu goma sha biyu, kewaye da shi.

  7. Sai Huram ya yi wani ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da ya kira Teku. Zurfin kwanon nan kamu bakwai da rabi, fāɗinsa kamu goma sha biyar, da’irarsa kuma kamu talatin ne.

  8. Sarki ya sa aka yi zubi a abin yin tubalin laka a filin Urdun, tsakanin Sukkot da Zaretan.

  9. Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda.

  10. Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.

  11. ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi?

  12. Sa’an nan ka sa tukunyan nan da babu kome a kan garwashi sai ta yi zafi har darmarta ta yi ja wur domin dattinta ya narke tsatsarta kuma ta ƙone.