Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Molding: Of images

5 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Of images

  1. Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”

  2. Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”

  3. “Kada ku yi alloli na zubi.

  4. “ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  5. Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”