Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Metals

41 ayoyi · 17 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sunan kogi na fari, Fishon. Shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.

  2. (Zinariyar wannan ƙasa kuwa tana da kyau, akwai kuma kayan ƙanshi da duwatsun da ake kira onis a can ma.)

  3. Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa.

  4. Sa’an nan ka sa kwaf nawa, wannan na azurfa a bakin buhun autan, tare da kuɗinsa na hatsi.” Sai mai hidimar ya yi kamar yadda Yusuf ya umarta.

  5. Amma ka hura numfashinka sai teku ya rufe su. Suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.

  6. Ka yi masa ƙaho a kowace kusurwan nan huɗu, domin bagade da ƙahoni duk su zama ɗaya, ka dalaye bagade da tagulla.

  7. Ka yi raga na tagulla dominsa, ka kuma yi zoben tagulla a kowace kusurwan nan huɗu na bagaden.

  8. Sa’an nan Eleyazar firist, ya ce wa sojojin da suka je yaƙi, “Wannan ita ce ƙa’idar da Ubangiji ya ba wa Musa.

  9. Zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, kuza, darma

  10. da dukan abin da wuta ba ta iya ci, dole yă shiga wuta sa’an nan zai zama da tsabta. Amma dole a kuma tsarkake ta da ruwan tsarkakewa. Duk abin da wuta za tă iya ci, dole a shigar da ita a ruwan tsarkakewa.

  11. “ ‘In wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, to, shi mai kisankai ne; sai a kashe mai kisankan nan.

  12. ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.

  13. Saboda haka ya mayar da azurfan wa mahaifiyarsa, ita kuwa ta ɗauki azurfa ɗari biyu na shekel ta ba wa maƙeri, wanda ya mai da su sura da kuma gunki. Aka kuwa sa su a gidan Mika.

  14. Sarki ya sa aka yi zubi a abin yin tubalin laka a filin Urdun, tsakanin Sukkot da Zaretan.

  15. Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara na mashigin gidan sarki.

  16. kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.

  17. Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya.

  18. Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.

  19. akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.

  20. Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.

  21. Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki.

  22. A maimakon tagulla zan kawo zinariya, azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe. A maimakon katako zan kawo tagulla, baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu. Zan sa salama ta zama gwamnarki adalci kuma mai mulkinki.

  23. Mazuga yana zuga da ƙarfi don yă ƙone dalma da wuta, amma tacewa yana tafiya a banza; ba a fitar da mugaye.

  24. “Ɗan mutum, gidan Isra’ila ta zama ƙwan maƙera a gare ni; dukansu tagulla ne, kuza, ƙarfe da darma da suka rage a tanderu. Su ƙwan maƙerar azurfa ne kawai.

  25. Kamar yadda mutane sukan tattara azurfa, tagulla, ƙarfe, darma da kuza a cikin tanderu don su narkar da su da wuta, haka zan tattara ku cikin fushina da kuma hasalata in sa ku cikin birnin in narkar da ku.