Skip to content

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen ’yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, “Na tsamo shi daga ruwa.”

  2. Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa.

  3. Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.”

  4. Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya.

  5. Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.

  6. Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa.

  7. Ana nan wata rana Musa yana kiwon tumakin Yetro surukinsa, firist na Midiyan, sai ya bi da tumaki zuwa gefe mai nisa a cikin hamada, har ya zo Horeb, dutsen Allah.

  8. Sai Musa ya ce, “Wannan abin mamaki ne, don me wannan itace bai ƙone ba? Bari in matso kusa in gani.”

  9. Da Ubangiji ya ga Musa ya matso don yă duba, sai Allah ya yi kira daga cikin ƙaramin itacen ya ce, “Musa! Musa!” Sai Musa ya amsa ya ce, “Ga ni.”

  10. Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.

  11. Amma Musa ya ce wa Allah, “Wane ni in tafi wurin Fir’auna, in kuma fitar da Isra’ilawa daga Masar?”

  12. Musa ya ce wa Allah, “A ce ma na tafi wurin Isra’ilawa na ce musu, ‘Allah na kakanninku ya aiko ni wurinku,’ in suka tambaye ni, ‘Mene ne sunansa?’ Me zan ce?”

  13. Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ ”

  14. Allah ya kuma ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Ubangiji, Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub, ya aiko ni wurinku.’ Wannan shi ne sunana har abada, sunan da za a tuna da ni daga tsara zuwa tsara ke nan.

  15. Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”

  16. Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi.

  17. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa.

  18. Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”

  19. Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka.

  20. Sai Musa ya koma wurin Yetro surukinsa, ya ce masa, “Bari in koma wurin mutanena a Masar, in ga ko da mai rai a cikinsu.” Yetro ya ce, “Tafi, ka kuma sauka lafiya.”

  21. Ubangiji ya riga ya gaya wa Musa a Midiyan, “Koma Masar, domin dukan mutanen da suke neman su kashe ka sun mutu.”

  22. Sai Musa ya ɗauki matarsa da ’ya’yansa maza, ya sa su a kan jaki, suka kama hanya zuwa Masar. Ya kuma ɗauki sandan Allah a hannunsa.

  23. Ubangiji ya ce wa Musa, “Bayan ka koma Masar, ka tabbata ka aikata dukan mu’ujizan da na sa cikin ikonka a gaban Fir’auna. Amma zan taurare zuciyarsa domin kada yă bar mutanen su tafi.

  24. Ubangiji ya ce wa Haruna, “Tafi cikin hamada ka sadu da Musa.” Sai ya sadu da Musa a dutsen Allah, ya sumbace shi.

  25. Sai Musa ya gaya wa Haruna dukan abin da Ubangiji ya aike yă faɗa, da kuma dukan mu’ujizan da ya umarce shi yă aikata.