Tsallake zuwa abun ciki

Moses

774 ayoyi · 7 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Moses

Tace bisa littafi
  1. Musa da Haruna suka tattara dukan dattawan Isra’ilawa,

  2. sai Haruna ya gaya musu dukan abin da Ubangiji ya ce wa Musa. Ya kuma aikata mu’ujizan a gaban mutanen,

  3. Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”

  4. Amma sarkin Masar ya ce wa, “Musa da Haruna, don me kuke hana mutane yin aikinsu? Ku koma wurin aikinku!”

  5. Da suka bar Fir’auna, sai suka sadu da Musa da Haruna suna jira su sadu da su,

  6. Musa ya koma wurin Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, don me ka kawo wahala a kan mutanen nan? Abin da ya sa ka aiko ni ke nan?

  7. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Yanzu za ka gan abin da zan yi da Fir’auna. Zan sa shi dole yă bar su su tafi, har ma yă iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”

  8. Allah ya kuma ce wa Musa, “Ni ne Ubangiji.

  9. Musa ya faɗa wa Isra’ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne a gare shi ba, don ɓacin rai saboda tsananin aikin bauta.

  10. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,

  11. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “In Isra’ilawa ba su ji ni ba, yaya Fir’auna zai ji ni, da yake ina magana da ƙyar?”

  12. Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna game da Isra’ilawa da Fir’auna sarkin Masar, ya umarce su su fitar da Isra’ilawa daga Masar.

  13. Amram ya auri ’yar’uwar mahaifinsa Yokebed, wadda ta haifa masa Haruna da Musa. Amram ya yi shekara 137.

  14. Wannan Haruna da Musa ne, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana ya ce, “Ku fitar da Isra’ilawa daga Masar ɓangare-ɓangare.”

  15. Su ne suka yi magana da Fir’auna sarkin Masar game da fitar da Isra’ilawa daga Masar, wannan Musa da Haruna.

  16. Ana nan, sa’ad da Ubangiji ya yi magana da Musa a Masar,

  17. ya ce masa, “Ni ne Ubangiji. Sai ka faɗa wa Fir’auna sarkin Masar kome da na faɗa maka.”

  18. Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, ina magana da ƙyar, ƙaƙa Fir’auna zai kasa kunne gare ni?”

  19. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Duba, na maishe ka kamar Allah ga Fir’auna, ɗan’uwanka Haruna kuma zai zama annabinka.

  20. Musa da Haruna suka aikata yadda Ubangiji ya umarce su.

  21. Musa yana da shekara tamanin da haihuwa, Haruna kuma yana da shekara tamanin da uku, sa’ad da suka yi magana da Fir’auna.

  22. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  23. Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji.

  24. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Zuciyar Fir’auna taurariya ce, ya ƙi yă bar mutanen su tafi.

  25. Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka ɗauki sandanka, ka miƙa hannunka kan ruwan Masar, kan kogunansu da rafuffukansu da kududdufansu da kuma dukan tafkunansu, za su zama jini.’ Jini zai kasance ko’ina a Masar, har ma a cikin abubuwan ajiyar ruwansu da aka yi da itace da kuma dutse.”