- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 1:1kusan 33 M.
A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar
- Ayyukan Manzanni 1:2kusan 33 M.
har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.
- Ayyukan Manzanni 1:3kusan 33 M.
Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.
- Ayyukan Manzanni 1:4kusan 33 M.
A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai.
- Ayyukan Manzanni 1:5kusan 33 M.
Gama Yohanna ya yi baftisma daruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
- Ayyukan Manzanni 1:6kusan 33 M.
Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”
- Ayyukan Manzanni 1:7kusan 33 M.
Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa.
- Ayyukan Manzanni 1:8kusan 33 M.
Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”
- Ayyukan Manzanni 1:9kusan 33 M.
Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.
- Ayyukan Manzanni 1:10kusan 33 M.
Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su.
- Ayyukan Manzanni 1:11kusan 33 M.
Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”
- Ayyukan Manzanni 1:12kusan 33 M.
Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin.
- Ayyukan Manzanni 1:13kusan 33 M.
Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.
- Ayyukan Manzanni 1:14kusan 33 M.
Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.
- Ayyukan Manzanni 1:15kusan 33 M.
A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin)
- Ayyukan Manzanni 1:16kusan 33 M.
ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu
- Ayyukan Manzanni 1:17kusan 33 M.
dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”
- Ayyukan Manzanni 1:18kusan 33 M.
(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo.
- Ayyukan Manzanni 1:19kusan 33 M.
Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)
- Ayyukan Manzanni 1:20kusan 33 M.
Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’
- Ayyukan Manzanni 1:21kusan 33 M.
Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu,
- Ayyukan Manzanni 1:22kusan 33 M.
farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”
- Ayyukan Manzanni 1:23kusan 33 M.
Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas.
- Ayyukan Manzanni 1:24kusan 33 M.
Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa
- Ayyukan Manzanni 1:25kusan 33 M.
ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.”