Skip to content

Paul

179 ayoyi

An kuma san shi da: Saul, Mercurius

Ayoyin da suka ambaci Paul

Tace bisa littafi
  1. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.

  2. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.

  3. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.

  4. Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist

  5. Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, “Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”

  6. Shawulu ya tashi daga ƙasa, amma sa’ad da ya buɗe idanunsa bai iya ganin wani abu ba. Saboda haka aka kama hannunsa aka yi masa jagora zuwa cikin Damaskus.

  7. Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.

  8. Sa’an nan Ananiyas ya tafi gidan ya kuma shiga ciki. Da ya sa hannuwansa a kan Shawulu, sai ya ce, “Ɗan’uwana Shawulu, Ubangiji, Yesu, wanda ya bayyana gare ka a kan hanya yayinda kake zuwa nan, ya aiko ni domin ka sāke gani a kuma cika ka da Ruhu Mai Tsarki.”

  9. bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.

  10. Duk da haka Shawulu ya yi ta ƙara ƙarfi, ya kuma rikitar da Yahudawan da suke zaune a Damaskus, ta wurin tabbatar musu cewa, Yesu shi ne Kiristi.

  11. amma Shawulu ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi.

  12. Da ya zo Urushalima, ya yi ƙoƙarin shiga cikin almajiran amma dukansu suka ji tsoronsa, ba su gaskata cewa tabbatacce shi almajiri ba ne.

  13. Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu,

  14. Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.

  15. Sa’ad da Barnabas da Shawulu suka kammala aikinsu, sai suka komo daga Urushalima, tare da Yohanna, wanda ake kira Markus.

  16. A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu.

  17. Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.”

  18. wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah.

  19. Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce,

  20. Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima.

  21. Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!

  22. Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.

  23. Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.

  24. Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai.

  25. Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.