Skip to content

Ephesus

17 verses

37.9500, 27.3600 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Ephesus

  1. Suka isa Afisa, inda Bulus ya bar Firiskila da Akwila. Shi kansa ya shiga majami’a ya kuma yi muhawwara da Yahudawa.

  2. Amma da yake barin wurin, ya yi alkawari cewa, “Zan dawo in Allah ya yarda.” Sa’an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

  3. Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.

  4. Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai,

  5. Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai.

  6. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan.

  7. Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, sa’an nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba tă san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba?

  8. Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos.

  9. Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya.

  10. In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai, “Sai mu ci mu sha, da yake gobe za mu mutu.”

  11. Sai dai zan kasance a Afisa har lokacin Fentekos,

  12. Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu.

  13. Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba

  14. Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.

  15. Na aiki Tikikus zuwa Afisa.

  16. wadda ta ce, “Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”

  17. “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.