Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Alexandria

4 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus,

  2. Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.

  3. A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki.

  4. Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus.